Politics
Ƙungiyar Atiku Kano Business Forum Ta Karɓi Baƙuncin ’Ya’yan Atiku Abubakar A Kano
Ƙungiyar Atiku Kano Business Forum ta karɓi baƙuncin ’ya’yan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, wato Alhaji Muhammad Atiku Abubakar da Alhaji Mustapha Atiku Abubakar, a Kano.
Ƙungiyar, ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar ɗinta na Kano, Alhaji Yusuf Yakubu Mai Leda, ta karɓi baƙuncin tawagar a ofishinta da ke Kano.
Jami’an Ƴansanda Sun Kama Mutane Biyu Kan Barazanar Sace Sarkin Ƙauye A Kano
Da yake tsokaci kan ziyarar, Alhaji Yusuf Yakubu Mai Leda ya bayyana cewa sun tattauna muhimman batutuwan da suka shafi ayyukan ƙungiyar da kuma dabarun ƙarfafa tafiyar siyasar Alhaji Atiku Abubakar gabanin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Ya ce tattaunawar ta mayar da hankali kan hanyoyin da ƙungiyar za ta bi wajen bunƙasa tafiyar da kuma tallafa wa burin Atiku Abubakar na samun nasara a zaɓen mai zuwa.
A yayin ziyarar, Alhaji Muhammad Atiku Abubakar da Alhaji Mustapha Atiku Abubakar sun samu rakiyar wasu mambobin tawagarsu.
A nasa ɓangaren, shugabannin da mambobin Atiku Kano Business Forum sun nuna farin cikinsu da ziyarar, inda suka yi musu kyakkyawar tarba.
Ƙungiyar ta bayyana aniyarta ta ci gaba da gudanar da ayyukan da za su ƙarfafa tafiyar siyasar Atiku Abubakar a Kano da sauran sassan Najeriya.

