Connect with us

News

“Ku Karɓi Kuɗinsu, Ku Kashe, Ku Zaɓi Wanda Kuka Ga Dama”  —Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Gwamnan Jihar Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM, Seyi Makinde, ya shawarci magoya bayan jam’iyyarsa da su karɓi kuɗin da ’yan siyasa ke ba su yayin kamfen, amma su yi zaɓe bisa ga ra’ayinsu.

Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin wani gangamin Yaƙin Neman Zaɓen shugaban ƙasa da jam’iyyar APM ta gudanar a Jihar Bauchi, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

An Kama Wani Mutum Bisa Zargin Jagorantar Masu Satar Wayoyi A Kano

Gwamnan ya ce bai kamata magoya bayansa su ji wani nauyin laifi ba idan suka karɓi kuɗin da ’yan siyasa ke ba su, matuƙar ba za su bari hakan ya rinjayi zaɓinsu ba.

A kalamansa, “Kada ku damu ko kaɗan. Idan suka kawo kuɗi, kuɗinku ne, ku karɓa. Amma ku yi zaɓe bisa ga ra’ayin zuciyarku. Kuma na san zuciyarku tana tare da mu da jam’iyyar APM.”

Makinde ya kuma yi alƙawarin sake fasalin tattalin arzikin Nijeriya, tsarin tsaro da kuma zamantakewar al’umma idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.

Advertisement

Ya buƙaci ’yan Nijeriya da ba su gamsu da yadda ƙasar ke tafiya a halin yanzu ba, da su mara wa shirinsa mai taken “Reset Nigeria” baya domin kawo sauyi a ƙasar.

A cewarsa, sake fasalin Nijeriya shi ne hanyar da za a bi wajen tunkarar matsalolin rashin adalci, rashin gaskiya da kuma gazawar gwamnati wajen magance ƙalubalen da al’umma ke fuskanta.

Ya kuma yi kira ga ’yan ƙasar da su kasance cikin waɗanda za su taka rawa wajen tabbatar da wannan sauyi.

A nasa jawabin, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar APM, Lawal Daura, ya bayyana cewa siyasar ƙarya, yaudara da munafurci na barazana ga dimokuraɗiyyar Nijeriya.

Ya ce an tsara shirin “Reset Nigeria” ne domin tunkarar waɗannan ƙalubale da kuma tabbatar da gaskiya da riƙon amana a harkokin mulki.

Shi ma shugaban jam’iyyar na ƙasa, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana cewa shirin APM ya ƙunshi hanyoyin magance matsalolin da Nijeriya ke fuskanta.

Advertisement

Bala Mohammed ya kuma bayyana goyon bayansa ga takarar Makinde, yana mai cewa gwamnan ya nuna ƙwazo wajen gudanar da ayyuka da kuma tafiyar da al’amura ba tare da nuna bambanci ba.

Gangamin ya samu halartar dimbin magoya bayan jam’iyyar da shugabanninta, waɗanda suka halarta sanye da tufafi masu launukan tambarin jam’iyyar APM.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending