Connect with us

News

An ceto sama da mutum 800 a ambaliya a Hadaddiyar Daular Larabawa

Published

on

Ambaliya a Dubai

DAGA Kabiru Basiru fulatan

 

 

 

Hukumomi a ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun ce tawagogin aikin agaji sun ceto fiye da mutum ɗari takwas sakamakon ambaliyar da mamakon ruwan sama ya janyo.

 

Advertisement

Kusan mutum dubu huɗu aka bai wa mafaka ta wucin-gadi a arewacin masarautun Fujairah da Sharjah.

Kotun majistre ta umarci matashi da ya share haraba bisa yunƙurin yin sata

 

Hukumomin Daular sun ce ruwan saman shi ne mafi ƙarfi da aka taɓa samu a Fujairah cikin shekara talatin.

 

A Iran ma ambaliya ta shafi ɗaruruwan ƙauyuka, lamarin da ya jawo rufe manyan hanyoyi.

Advertisement

 

Kafar yaɗa labaran ƙasar Iran din ta ce mutum goma ne suka rasa rayukansu a yankin Firouz Kooh da ke arewa maso gabashin Tehran, sannan mutum goma sha shida sun ɓata.

 

Masu aikin ceto na ci gaba da neman waɗanda ake sa ran suna da sauran kwana.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending