News
Babban Hafsan Sojin Najeriya Ya Sanar Da Ƴan Ta’adda Cewa Karshen Su Ya Zo
Daga kabiru basiru fulatan
Babban Hafsan Sojojin Kasa na Nijeriya, Laftanal Janar Farouk Yahaya a wani martani da ya mayar kan ta’asar da ‘yan ta’adda da sauran masu daukar makami suke yi a kasar nan, ya bayyana cewa karshensu ya zo.
Ya yi wannan gargadin ne a yayin da ya ziyarci Maiduguri domin kara zaburad da sojojin da ke fatattakar ‘yan ta’addan boko haram da kuma kaddamar da wasu manyan ayyuka na ci gaba da aka aiwatar domin kyautata jin dadin sojojin da ke fagen daga.
An kori minista a Ghana bayan ta shafe tsawon lokaci ba ta zuwa wajen aiki
Wannan sako ne ga dukkan masu aikata miyagun laifuka, walau suna tsara bidiyo su watsa ko ma dai me suke yi, karshensu ya zo kuma za mu cimma su da yardar Allah.”
Laftanar Janar Yahaya ya kara da cewa, ‘yan fashin daji, da ‘yan boko haram da sauran masu aikata miyagun laifuka ba za su tsira ba, kana ya yi alkawarin cewa babu wanda zai samu mabuya a cikinsu.
Kazalika Babban Hafsan Sojin ya ce duk wani mutum da yake daukar makami don ya yaki Nijeriya a kan kowane irin dalili ya shirya fuskantar fushin doka.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
