Connect with us

News

Mukaddashin firaministan Iraƙi ya roƙi masu zanga-zanga su kwantar da hankulansu

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Mukaddashin firaministan Iraq, Mustapha al-Khadimi, ya yi kira da a kwantar hankula bayan magoya bayan malamin nan mai karfin fada aji a kasar Moqtada al-Sadr sun farma majalisar dokokin kasar karo na biyu a cikin mako guda.

Advertisement

Magoya bayan malamin da ke zaman dirshan a ginin majalisa da ke Bagadaza, na nuna adawarsu da zabin da aka yi wa wani mai goyon bayan Iran a matsayin dan takarar firaminista.

A bi a hankali wajen neman tsige Buhari, In ji Kwankwaso

Advertisement

A jiya Asabar, an raunata mutane fiye da 120 a yayin zanga-zangar da aka yi a titunan birnin.

Wasu masu zanga zangar sun janye shingayen da aka sanya na kariya a wata gunduma mai suna Green Zone.

Advertisement

Hadakar jam’iyyar Mr Sadr ta samu rinjaye a mafi yawan kujerun majalisar a zaben da aka yi a watan Oktoban da ya wuce, to amma sun janye daga majalisar saboda kiki-kakar siyasa.

BBC NEWS

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending