Connect with us

News

Kwamishinan matasa da wasanni na jahar yobe ya rasu

Published

on

Daga Yasir sani Abdullahi

Goni Lawal, Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Yobe ya rasu.

Jaridar The Cable ta rawaito cewa Tijjani Ciroma, kakakin ma’aikatar ne ya tabbatar da hakan a yau Laraba.

Ya ce Lawal ya rasu ne a wani haɗarin mota da ya rutsa da su a hanyar Potiskum zuwa Azare da misalin karfe 7:30 na yammacin jiya Talata.

Ciroma ya ce marigayin, mai shekaru 57 a duniya yana kan hanyarsa ta zuwa Kano ne domin shiga jirgi zuwa Abuja domin gudanar da aikinsa.

Kakakin ya ce za a yi sallar jana’izar marigayin da misalin karfe 11 na safe a Cibiyar Musulunci ta Yobe da ke Damaturu.

Advertisement

An naɗa Lawal a matsayin Kwamishina a 2019.

Ya kasance mamba na majalisar wakilai

Kuma ya rasune a Wani asibiti dake dake potiskun a jahar ta yobe


 

 

 

Advertisement

 

 

 

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending