Connect with us

News

Yan sanda sun kama wanda ake nema ruwa a jallo, Rasheed Okoilu, a Osogbo

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

 

 

Advertisement

Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta ce ta kama wani shahararren mai kisan gilla da ake nema ruwa a jallo, Rasheed Hamed, wanda aka fi sani da Rasheed Okoilu da sanyin safiyar Lahadi.

 

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a garin Osogbo, inda ya ce, rundunar ‘yan sanda ta hadin guiwa da jami’an ‘yan sanda daga ofishin ‘yan sanda na Dugbe da kuma ofishin ‘yan sanda na Oke Baale tare da goyon bayan mafarautan yankin sun cafke wanda ake zargin.

Ban taba bakin ciki ko nadama don an cire ni daga sarkin Kano ba — Sanusi II

Ms Opalola, Sufeto na ‘yan sanda, ta ce an bi diddigin wanda ake zargin tare da kama shi bayan da ya yi kisan kai a Egbatedo, Osogbo, inda ya kashe mutane uku.

 

Advertisement

 

Ta ce an mika wanda ake zargin ga sashin yaki da ayyukan asiri na rundunar ‘yan sanda a jihar kuma ana kan gudanar da bincike.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya tuna cewa, a ranar 10 ga watan Maris ne rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta bayyana Rasheed Okoilu da wani Solomon Adedimeji (Solo Iwara) da ake nema ruwa a jallo bisa laifukan kisan kai, kone-kone, kashe-kashen al’ada, fashi da makami, fyade da kuma garkuwa da mutane.

 

Rundunar ‘yan sandan ta yi gargadin cewa duk wanda ya ajiye wadanda ake zargin za a dauke shi a matsayin wanda ke da hannu wajen aikata laifukan da suka aikata.

 

Advertisement

Sai dai rundunar ‘yan sandan ta yi alkawarin baiwa duk wanda ya samu bayanai masu amfani ga inda mutanen da ake nema suke, za su ba su kyauta mai kyau.

 

DAILY NIGERIAN

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending