News
Ecowas ta dakatar da daukar ma’aikata saboda zargin wariya
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Kungiyar raya kasashen yammacin Afirka – ECOWAS ta dakatar da daukar ma’aikata.
Kakakin majalisar dokokin kungiyar, Mr. Sidie Tunis, ne ya bayar da umarnin yana mai cewa matakin zai soma aiki nan take.
An bayar da umarnin ne bayan zargin da tawagar Najeriya ta yi cewa an nuna wa masu neman aiki daga ƙasar wariya a wajen daukar aiki da kuma ƙarin girma.
Masu wakiltar Najeriya a kungiyar ta ECOWAS sun kuma yi barazanar janyewa daga ƙungiyar da kuma daina ba da ƙudade domin raya ƙungiyar.
Sun zargi cewa akwai manyan ma’aikata a kungiyar da ke daukar ‘yan uwansu da mutanen da ransu yake so ba bisa ƙa’ida ba.
Advertisements
