Sports
Luka Modric ya nemi ƙarin hazakar abokan wasansa bayan tafiyar Casemiro
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Real Madrid ta lallasa Celta Vigo da ci 4-1 a daren ranar Asabar, inda Luka Modric ya ci gaba da zama babban dan wasan tsakiya. Da alama dai ba a samu canji sosai ba, tun bayan da aka sanar da tafiyar Casemiro zuwa Manchester United a wannan lokacin.
Duk da haka gwarzon dan wasa na Croatia ya yi imanin cewa rashinsa tabbas za a ji. Modric, Casemiro da Toni Kroos sun kafa tushen nasarar Real Madrid a gasar zakarun Turai a cikin shekaru goma da suka gabata.
Da yake magana da DAZN bayan nasarar akan Celta, Modric ya koka da ficewarsa. Wasannin mu sun dauki hazakarsa.
“Abin da Casemiro ya yi abin burgewa ne, mun kafa tarihi tare da shi, ya kasance muhimmin dan wasa a gare mu kuma za mu yi kewarsa da yawa, a matsayinmu na yan wasa da kuma zaman takewar mutum.”
“Wannan wani bangare ne na kwallon kafa, na yi bakin cikin ganin ya tafi amma dole ne mu ci gaba da tafiya ba tare da shi ba kuma kowane dan wasa dole ne ya ba da karin hazaka dangane da abubuwan da ya yi.”
Yadda Carlo Ancelotti zai tunkari rashin Casemiro abu ne mai ban sha’awa a La Casa Blanca.
A karawar da Celta Aurelien Tchouameni, wanda aka yiwa lakabi da sabon Casemiro wanda zai maye gurbinsa na dogon lokaci, ya zo a tsakiyar inda dan kasar Brazil ke bugawa tare da Eduardo Camavinga.
Wasu kuma sun ba da shawarar cewa Fede Valverde na iya komawa tsakiyar daga bangaren dama ko ma David Alaba na iya ci gaba da taka leda a gurbin.
