Connect with us

News

Akwai Hannun Yan Kasashen Waje A Matsalar Tsaron Najeriya—- Sabon Kwanturolar Hukumar Shige da Fice, Shiyyar Kaduna

Published

on

Immigration

 

Daga: Muslim yunus Abdullahi

 

 

 

 

Advertisement

 

 

 

Kwanturola Liman Sani Kila ya koma matsayinsa na sabon Kwanturolar Hukumar Shige da Fice ta Kasa, shiyyar jihar Kaduna.

Kwanturola Liman wanda ya koma bakin aiki a wannan makon, ya umurci jami’ai d da su ci gaba da aiki yadda ya kamata, yayin da ya yi alkawarin karfafa hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro a jihar da nufin dakile safarar mutane a jihar.

A cewarsa, lamarin ba zai kasance kamar yadda aka saba ba, inda ya kara da cewa, “a matsayina na sabon Kwanturolan hukumar shige da fice ta jihar Kaduna, zan kara hada kan kokarin da Kwanturola na baya, tare da yin aiki tare da sauran hukumomin tsaro. ”

Advertisement

A cewarsa, galibin hare-haren ‘yan bindiga a fadin kasar nan ‘yan kasashen waje ne ke haddasa su. Kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito

Da yake zantawa da ‘yan jarida jim kadan bayan taron ranstar da shi, Kwanturola Liman ya tunatar da jami’an hukumar cewa, hukumar shige da fice a Kaduna tana da wani sashe da aka riga aka kafa a shiyyar da ke aiki da kungiyar ECOWAS ke da alhakin ba da izinin zama ga baƙi zuwa cikin jihar, kamar yadda sashe na 2 na Dokar Shige da Fice ta shekarar 2015 ya ba da dama.

Ya kara da cewa jami’an rundunar ‘yan sanda na “Operation Yaki’ na aiki da hukumar domin duba ayyukan ‘yan ci-rani a kan iyaka, a matsayin babban nauyin da ya rataya a wuyansu.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending