News
Fadar shugaban kasa ta caccaki gwamnan jahar benuwe Samuel ortom
Daga Yasir sani Abdullahi
Fadar shugaban kasa ta mayar da martani a kan ikirarin da gwamnan jihar Binuwai Samuel Ortom ya yi, yayin hira da wata kafar yada labarai cewa wani babban jami’in tsaro ya sanar da shi cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaron kasar, a kan kada su dauki matakin murkushe Fulani makiyaya, da ake zargin su na da hannu a tashin hankalin baya baya nan.
A bayanne ta ke cewa Fadar shugaban kasa bata ji dadin kalaman da suka fito daga bakin gwamnan ba .
Kakakin fadar Shugaban kasa Garba Shehu ya bayyana kalaman nasa a matsayin maganar da ba ta da tushe balantana makama.
Ya kuma kalubanci gwamnan a kan ya bayyana sunayen jami’an tsaron da suka fada masa haka.
Idan ya Isa shi jarumine tom ya bayyana mana sunan jami,in sojan da yabashi wannan labarinn kamar yadda yayi ikirari da farko ko Kuma yayi shiru da bakin sa
Fadar shugaban kasan tace kasar na fama da tashe tashen hankula adan haka bai kamata ace wasu Yan siyasa su Dunga bada irin labarukann ba Dan raba kan Al, umma
