News
Ambaliyar ruwa na ci gaba da ɗaidaita Pakistan
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Kudancin Pakistan na fuskantar barazanar karin ambaliyar ruwa a yayin da ruwa ke gangarowa daga kogin Indus wanda mamakon ruwan saman ya cika shi makil.
Fiye da mutane dubu daya da dari daya ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwan da ta shafi kaso daya bisa uku na kasar.
Breaking news EFCC ta kama kakakin majalisar Ogun a filin jirgin saman Legas
Wakiliyar BBC ta ce jami’ai a kasar sun ce mutune miliyan 1 da dubu dari biyu sun rasa muhallansu a gundumar Daadu, sannan sojoji na aikin kwashe wadanda ambaliyar ta shafa a yankin, yayin da kai kayan agaji yanki ke fuskantar tarnaki.
Tuni Majalisar Dinkin Duniya ta nemi tallafin dala miliyan 160 don taimaka wa mutane fiye da miliyan shida da suke matukar bukatar taimakon gaggawa ciki har da samar da tsaftataccen ruwan sha da abinci da kuma wuraren zama.
Tun bayan fara mamakon ruwan sama a watan Yuni, Pakistan ke fama da ruwan sama kamar da bakin kwarya wanda kasar ta jima bata ga irinsa ba.
