Connect with us

News

Waye zai maye gurbin Shekarau a takarar Sanata ta NNPP?

Published

on

NNPP

Daga Yasir sani abdullahi

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

A farkon makon da muke ciki ne Sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari, tare da aikewa da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC takardar ajiye takarar Sanatan Kano ta tsakiya da yake a jam’iyyar, bisa zargin rashin adalci da yake ga jagoran jam’iyyar na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Advertisement

Tun bayan faruwar lamarin, al’umma ke tofa albarkacin bakinsu akan wanda ya kamata ya gaji wannan takara, musamman tsohon dan takara, Aliyu Sani Madaki, wanda kwankwasiyya ta tsayar a kakar zaben shekarar 2019 da ya gabata.

Hal ila yau, akwai masu fatan Sanata Rufai Sani Hanga ya samu wannan tikiti, akwai masu ganin Sha’aban Ibrahim Sharada ya ajiye takararsa ta gwamna a ADP domin yazo NNPP a bashi wannan tikiti, da sauran mutane da masoya ke musu fatan alheri.

Advertisement

Bisa doka, jam’iyya na da kwanaki 14 ne daga ranar da dan takara ya tura takardar ajiye takara ga INEC, daga nan kuma sai a shirye sabon zaɓen fidda gwani, duk cikin kwanaki 14.

A yanzu dai abin jira a gani, shi ne lokaci, domin bayyana wanda zai samu wannan tikiti cikin mutanen da ake yiwa zawarci.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending