An kama jami’an lafiya uku a kasar Senegal kan zargin sakaci da aiki bayan mutuwar wata mai jego da jaririnta lokacin da aka yi mata tiyatar haihuwa.
Kungiyar jami’an lafiya ta ce wadanda aka kama sun hada da likitan mata, da mai yin allura kafin aikin tiyata da wata malamar jinya.
An kai kwana 200 da fara yajin aikin malaman jami’o’i a Najeriya
Matar ta gamu da ajalinta sakamakon zubda jinin da ta yi fiye da kima, ya yin jaririn ya mutu saboda raunukan da aka ji ma sa lokacin tiyatar haihuwar.
Kungiyar likitocin mata da na fida a Senegal, sun kare mutane ukun tare da sukar kamasu da aka yi da cewa sam bai dace ba.
A wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na AFP ya fitar, na cewa sun yi ikirarin likitocin sun dauki matakin da ya dace akan matar da jaririn.
A shekarar da ta gabata, sai da shugaba Macky Sall ya bada umarnin yin garanbawul a fannin lafiyar Senegal, sakamakon korafe-korafe mutane kan yawaitar mutuwar mata masu juna biyu lokacin haihuwa.
Lamarin ya hada da wasu ma’aikatan jinya uku, da aka samu da laifin kin taimakawa mace mai nakuda a lokacin da ta ke cikin matsanancin hali.
