Sports
Ahmad Musa ya sauya sheƙa zuwa ƙungiyar Sivasspor
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ɗan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagle Ahmad Musa, ya sauya kungiyar kwallon kafa bayan da
wa’adin sa ya kare a tsohuwar kungiyar sa na shekara biyu.
Ahmad Musa Mai shekaru 29 ya rattaba hannu a jiya juma’a na tsawon shekara biyu a babbar ƙungiyar ta ƙasar Turkiyya, wadda take buga ajin kwararru a Turkish super Lig.
Ƙarin mutum 173 sun kamu da korona a Najeriya
Ƙungiyar ta nuna kwadayin ta akan gogewar dan wasan Ahmad Musa.
Shugaban kungiyar mecnun otyakmaz ya tabbatar da ɗaukar ɗan wasan na tsawon kwantiragin shekara biyu.
Advertisements
