Connect with us

News

Wasu ‘Yan Siyasa Na Daukar Zaben 2023 Na Ko A Mutu, Ko A Yi Rai –INEC

Published

on

DAGA MUSLIM YUNUS ABDULLAH 

 

 

 

 

 

Advertisement

 

Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta bayyana damuwar ta a kan yadda wasu ‘yan siyasa ke daukar zaben shekara ta 2023 a matsayin na ko a mutu ko a yi rai.

 

Jami’an hulda da jama’a na hukumar Festus Okoye ya bayyana haka a Abuja, yayin kaddamar da tawagar tattauna rikicin zabe da cibiyar bankasa harkokin dimokuradiyya CDD ta shirya.

Nasa ta sake soke ƙudirin harba gagarumin kumbo zuwa duniyar wata karo na biyu cikin mako ɗaya

Ya ce hukumar zabe ta na jin dadin yadda ‘yan jarida ke watsa labarum ta, amma ya dace a rika samun sahihan labarai daga gare ta ta hanyar tuntubar ta.

Advertisement

 

Festus Okoye, ya ce Hukumar zabe ta na da kyakkyawar alaka tsakanin ta da ‘yan jarida wajen bayyana wa al’umma labarun ta, amma ana samun labarun karya da ake yada wa mutane.

 

Ya ce kamar yadda su ke samun karuwar labarun karya da ake jingina wa hukumar, sun dauki matakin yaki da lamarin ta hanyar tsaftace labarun harkokin siyasa musamman ga wadanda su ka tsaya takara.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending