Connect with us

News

Yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya da dama a jihar Ondo

Published

on

Yan bindiga

DAGA KHADIJA ABDULLAHI MUHMD

 

 

Advertisement

 

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya da dama a kan babbar hanyar Benin zuwa Owo a karamar hukumar Ose da ke jihar Ondo ta Najeriya.

Advertisement

Jaridar Daily Trust ta ambato wata majiya na shaida mata cewa matafiyan na cikin wata babbar motar bas ne da ta taso daga jihar Edo zuwa jihar Ondo da ke kudu maso yammacin kasar.

DA ƊUMI-ƊUMI: FG ta dakatar da ƙarin harajin kiran waya

Advertisement

A yayin da take tabbatar da lamarin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ondo, Funmilayo Odunlami, ta ce ba za ta iya tabbatar da adadin mutanen da lamarin ya rutsa da su ba.

To amma ta ce tuni jami’an tsaron kasar suka fara bincike domin gano tare da kubutar da mutanen.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending