Connect with us

News

Gwamnatin tarayya ta toshe asusun banki 600 da kwace motocin alfarma 249

Published

on

Advertisements
ads

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADEEN

 

 

 

 

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kwace kadarori akalla 286 da asusun banki 600 na wasu mutane da ke tu’amalli da kwayoyi tsakanin watan Janairun 2021 zuwa Agustan 2022.

Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi wanda ya bayyana hakan wa manema labarai jiya Talata, ya ce kadarorin da aka kwace sun hada da motocin alfarma 249 da manyan gidaje 37.

Advertisement

FG: ta karbi harajin N127.03bn daga kira, SMS

Hukumar ta NDLEA ta bayyana a cikin kundin cewa tana kokari wajen ganin ta taka burki ga masu tu’amalli da kwayoyi a cikin kasar da suka kai kashi 14.4.

Babafemi ya ce a cikin watanni 20 da suka gabata, hukumar ta kwace motocin alfarma 249 da kadarori 37 a sassan kasar daban-daban.

Hukumar ta kuma ce ta yi nasarar kwace kudade da ke da alaka da kwayoyi da ya kai naira miliyan 619.

BBC NEWS

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending