News
Saudiyya na son daukar nauyin bikin baje-koli na 2030
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wakilan kasar Saudiyya sun gabatar da takardar neman daukar nauyin bakuncin babban bikin baje-koli na duniya da za a gudanar a shekarar 2030.
Wakilan kasar sun gabatar da kudurin ne ga shugaban hukumar da ke shirya bikin Dimitri Kerkentzes, a birnin Paris.
Ana son dakatar da shugabannin kananan hukumomi 15 a jihar Naija .
Kawo yanzu dai kasashe hudu ne suka gabatar da kudurinsu na neman daukar nauyin bakuncin bikin, wadanda suka hadar da Jamhuriyar Koriya da Ukraine, Italiya da kuma kasar Saudiyya.
Za dai a gudanar da babban bikin baje-koli na duniyar tsakanin daya ga watan Oktoban 2030 zuwa daya ga watan Afrilun 2031
BBC NEWS
Advertisements
