Connect with us

News

Shugaban Kwamitin Amintattu Na PDP Ya Yi Murabus

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAH 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Shugaban Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar PDP, Sanata Walid Jibril ya yi murabus daga mukaminsa.

 

Advertisement

Sanata Walid Jibril ya sauka daga kujerar tasa ce ranar Alhamis, a daidai lokacin da jam’iyyar ke fama da rikicin da take kokarin dinkewa.

QApple ya fitar da iPhone 14

Advertisement

 

Ya bayyana cewa ya yi murabus ne domin kauce wa kazancewar matsalar da kuma tabbadar da ganin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar ya lashe zaben 2023.

Advertisement

 

Jam’iyyar PDP da Atiku na tsaka mai wuya, a kokarinsu na dinke barakar da biyo bayan zaben Atiku a zaben dan takarar shugaban kasar jam’iyyar.

Advertisement

 

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, wanda shi ma ya yi zawarcin kujerar ya bayyana bacin ransa kan yadda Atiku ya zabi Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takarsa.

Advertisement

 

A yayin da Atiku da jam’iyyar ke kokarshin shawo kansa, Wike dai ya ki bayar da kai bori ya hau.

Advertisement

 

Bai tsaya nan ba, ya yi kira da Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Sanata Iyiorchia Ayu ya yi murabus daga mukaminsa, wanda shi kuma ya ce ba za ta sabu ba.

Advertisement

 

A gefe guda kuma ana zargin Wike da yunkurin goyon bayan ’yan takarar shugaban kasan jam’iyyun APC mai mulki, Bola Tinubu da kuma dan takara Jam’Obi.q@r Leba, Peter Obi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending