Connect with us

News

Ambaliya Ta Raba Kwaltar Titin Bursari Zuwa Damaturu Gida Biyu a Jihar Yobe

Published

on

DAGA IDIRS HUSSAINI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Titin wanda shi ya hade karamar hukumar Bursari da Tarmuwa da wasu kananan hukumomi har zuwa birnin Damaturu ya katse sakamakon wani ruwa maikarfi da ya dauki tsawon lokuta ana yi.

Advertisement

Shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa (SEMA) ta jihar Yobe ta jihar Alh. Muhammad Goje yace shugabanin kananan hukumomin na Bursari da Tarmuwa ne suka sanar da SEMA mawuyacin halin da jama’a suke ciki sakamakon ambaliyar.

Lewandowski zai fuskanci Bayern Munich

Advertisement

Ya kara da cewa “ruwan ya yi barna a Dapchi hedikwatar mulki na Bursari da kuma garin na Tarmuwa, kuma tuni suka fara shirin kai dauki cikin gaggawa domin taimakawa al’ummar yankin.

Alh. Muhammad Goje ya karkare da shawartar a’lummun da ke zaune yankin bakin tafkuna da su fara kaura zuwa gurare mara hatsari don gujewa fadawa irin wannan ibtila’i.

Advertisement

Shima a nashi bangaren shugaban Hukumar Lafiya a Matakin farko Dr. Babagana Kundi Machina ya yi kira ga al’ummar jihar da su tsabtace muhallan su domin gujewa kamuwa da cuttuka irin su kolara da makamantan su.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending