Sports
Kante da Mendy ba za su buga wa Chelsea gasar Zakarun Turai ba
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
Golan Chelsea Edouard Mendy da dan wasan tsakiyarta N’Golo Kante ba za su buga wasan Zakarun Turai da kungiyar za ta buga da RB Salzburg ba a birnin London.
Chelsea za ta karbi bakuncin Salsburg a Stamford Bridge, bayan rashin nasara a hannun Dynamo Zagreb, a wasan farko na rukunin E, wanda hakan ya yi sanadin sallamar tsohon kocin kungiyar Thomas Tuchel.
An dage bude makarantu a Sudan saboda ambaliya
Kante na fama da ciwo a cinyarsa, yayin da Mendy ke fama da ciwo a gwuiwarsa.
Sai dai Chelsea na da isassun yan wasa da za su maye gurbin masu raunin.
Shi ne wasa na farko da sabon kocin kungiyar Graham Potter zai jagoranta tun bayan nada shi makon da ya wuce.
An dage wasannin gasar Premier League na makon da ya wuce saboda jimamin mutuwar Sarauniya Elizabeth ta II, wanda hakan ya kawo jinkirin ganin kamun ludayin Potter a Chelsea.
