Sports
Real ta ci RB Leipzig wasa na biyu a jere a Champions League
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADEEN
Real ta ci kwallon ta hannun Fede Valverde, saura minti 10 lokaci ya cika a karawar da suka yi a Santiago Bernabeu.
Daf da za a tashi wasa Real ta kara na biyu ta hannun Marco Asensio da hakan ya sa ta hada maki ukun da take bukata a wasan.
Wannan shi ne karon farko da Real Madrid da RB Leipzig suka fafata a Gasar Zakarun Turai a tsakaninsu.
Real ta je ta doke Celtic 3-0 a wasan farko a cikin rukuni a makon jiya, ita kuwa
RB Leipzig ta sha kashi a gida a hannun Shakhtar Donetsk da ci 4-1.
‘Yan wasan da Carlo Ancelotti ya fuskanci Leipzig da su
‘Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Luis López.
Masu tssaron baya: Carvajal, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Rüdiger da kuma F. Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni da kuma D. Ceballos.
Masu cin kwallaye: Hazard, Asensio, Vini Jr., Rodrygo da kuma Mariano.
Sakamakon wasannin da aka buga ranar Laraba
-
News4 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News6 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
