Connect with us

News

ASUU: Gwamnatin Kaduna ta gargadi kungiyar daliban Najeriya kan rufe hanyar Kaduna-Abuja

Published

on

El Rufa.i

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Gwamnatin jihar Kaduna da ke Najeriya ta gargadi Kungiyar dalibai ta kasar da kada ta toshe hanyar Kaduna zuwa Abuja kamar yadda ta shirya.

Kwamishinan Tsaro da Lamuran Cikin Gida, Samuel Aruwan, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce “ba za mu amince da matakin daliban ba, don karya doka da oda ne.”

Sanarwar ta kara da cewa lamarin ka iya haifar da tashin hankali don haka ta gargadi ‘yan jihar da kada su sa kansu a cikinsa.

Rahotanni sun nuna cewa daliban na nuna fushinsu ne kan watanni bakwai da aka shafe ana yajin aikin malaman jami’o’i, wanda hakan ya sa kungiyar daliban ta yanke hukunci datse manyan hanyoyin sufuri, ciki hadda titin da ya tashi daga Kaduna zuwa Abuja, da kuma filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja har sai an biya musu bukatunsu.

Advertisement

Ko a ranar Litinin sai da daliban su ka toshe hanyar da ke zuwa filin jirgin Murtala Muhammad da ke Legas, lamarin da ya haifar da rudani da soke tashin wasu jiragen sama, kasancewar fasinjoji sun shafe sama da awa takwas a cunkoson motoci.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending