Connect with us

News

Kotu ta umarci ASUU ta koma bakin aiki

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

 

 

Advertisement

 

Kotun Ma’aikata ta Kasa ta umarci kungiyar malaman jami’o’i ta janye yajin aikin da take yi.

 

Da yake gabatar da hukunci kan bukatar wucin gadi da gwamnatin tarayya ta nema, Mai shari’ah Polycarp Hamman ya hana kungiyar ASUU ci gaba da yajin aiki har zuwa lokacin yanke hukunci kan shari’ar.

ASUU: Gwamnatin Kaduna ta gargadi kungiyar daliban Najeriya kan rufe hanyar Kaduna-Abuja

A farkon watan nan ne gwamnatin ta gurfanar da ASUU a gaban kotun kan yajin aikin da ta kwashe wata bakwai tana yi.

Advertisement

 

 

Mai shari’ah Polycap Hamman, wanda alkali ne da ke sauraron shari’ah a lokacin da kotun ke hutu ya kuma mayar da karar zuwa ga shugaban kotun ma’aikata don ya sake bai wa wani alkali wannan shari’ah. Ma’aikatar kwadago ta kasar ta ce gwamnati ta dauki mataki ne bayan tattaunawa da kungiyar malaman jami’o’in ta ci tura. A zamanta na farko, kotun karkashin jagorancin mai shari’a, Polycarp Hamman ta dage sauraren karar zuwa yau Laraba bayan ta saurari bayanai daga wurin masu shigar da kara da wadanda aka shigar kara. Gwamnatin tarayya tana son kotun ta bayyana halarci ko haramcin yajin aikin na ASUU.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending