News
Ba mu da shirin tayar da hatsaniya a zaben 2023 – IPOB
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kungiyar masu neman kafa jamhuriyar Biafra a yankin kudancin Najeriya (IPOB) ta ce taba da shirin kawo hatsaniya a yayin zaben 2023 mai zuwa a yankin Igbo.
Sakataren yada labaran kungiyar Emma Powerful ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, yana cewa babu kamshin gaskiya a cikin rahotannin da ke yawa cewa IPOB na shirin tayar da hankali a lokacin zaben 2023 a yankin kasar Igbo.
Farashin Abinci Ya Ragu A Duniya In Ji Majalisar Dinkin Duniya
Maimakon haka kungiyar ta zargi gwamnatin tarayya da kitsa matsalar tsaro a yankin kudu maso gabas, domin jefe firgici da kuma zargin mambobinsu da wannan aiki.
A kusan nan dai an ga hoton bidiyon wani mamban kungiyar Mr Simon Ekpa da ya yi ta yawo a intanet, inda yake cewa kungiyar ba za ta tabari a gudanar da zabe ba a yankin Biafra.
BBC
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
