News
Wani magidanci ya kashe matarsa ta hanyar lakada mata duka a Ogun Police
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
‘Yan sandan Jihar Ogun sun kama wani mutumi mai shekara 51, mai suna Oluranti Badejo, saboda zargin kashe matarsa, Folasade Badejo, bayan lakada mata duka.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a garin Orimerunmu, Mowe da ke karamar hukumar Obafemi-Owode na jihar ta Ogun.
Kotu Ta Saki Shugaban IPOB Nnamdi Kanu
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya fadawa manema labarai cewa an kama wanda ake zargin ne bayan kai musu rahoto da kanwar marigayiyar ta yi.
A cewar Abimbola, kanwar mamaciyar ta fada musu cewa ‘yar karamar sabani ne ta shiga tsakaninsu da kuma ya kai ga mijin lakadawa matarsa duka har ya yi sanadiyyar mutuwarta.
“A lokacin da ya gano cewa matarsa ta mutu, ya yi amfani da dutsen guga wajen kona wasu sassan jikin marigayiyar saboda a ce wutan lantarki ne ya kasheta, sai dai, bai san cewa karamar ‘yar su mai shekara takwas na kallonsa lokacin da yake aikata hakan,” in ji Oyeyemi.
A yanzu dai ana tsare da wanda ake zargin a sashen masu aikata laifin kisa na rundunar ‘yan sanda jihar ta Ogun, inda ake ci gaba da bincike
BBC
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
