Connect with us

Sports

Yan wasa 10 a Real Madrid sun lashe Ballon d’Or

Published

on

Ballon d'Or

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Ranar Litinin Karim Benzema dan kwallon tawagar Faransa ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya da ake kira Ballon d’Or na 2021/22.

 

Advertisement

Dan wasan na Real Madrid shi ne na baya-bayan nan da ya lashe kyautar daga kungiyar Santiago Bernabeu a bikin da French Football kan gudanar.

 

Advertisement

Kyauta ita ce ta 66 da aka yi bikin karrama ‘yan wasan tamaula da suka yi fice a duniya da aka yi a Faransa.

 

Advertisement

A karon farko an auna kwazon dan wasa bisa bajintar da ya yi a kakar tamaula, maimakon shekara daya da ake yi a baya.

 

Advertisement

Na Dukufa Wajen Magance Tsadar Kayan Abinci —Buhari

 

Advertisement

Benzema ya zama na 10 da ya lashe Ballon d’Or daga Real Madrid, bayan da Luka Modric ya dauka a 2018 daga kungiyar.

 

Advertisement

Alfredo Di Stéfano shi ne na farko da ya fara lashe kyautar daga Real Madrid a 1957, sannan ya kara zama zakara a 1959.

 

Advertisement

Raymond Kopa, wanda ya taka leda tare da Di Stéfano, shi ne ya lashe kyautar 1958 na biyu daga Real Madrid, sannan Stefanano da ya dauka karo na biyu a 1959.

 

Advertisement

Sauran ‘yan wasan da suka lashe Ballon d’Or a Real Madrid sun hada da Zinedine Zidane a 1998, wanda ya karba daga hannun Ronaldo Nazario na Inter Milan, wanda ya lashe a 1997 da kuma a 2002, wanda ya zama zakara a Real Madrid. Figo ya dauki Ballon d’Or a Real a 2000, sai Michael Owen a 2001 da Cannavaro a 2006 da kuma Kaka a 2007.

 

Advertisement

Shi kuwa Cristiano Ronaldo Ballon d’Or  sau biyar ya dauka a tarihin tamaularsa guda hudu a Real Madrid da daya a Manchester United a 2008

 

Advertisement

Kyaftin din tawagar Portugal wanda ke wasa a Old Trafford yanzu haka ya lashe a 2013 da 2014 da 2016 da kuma 2017.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending