Connect with us

News

Zan kammala aikin wutar mambilla idan na zama shugaban kasa – Tinubu

Published

on

Bola Tinubu

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin shawo kan matsaloli da ke arewacin Najeriya ke fuskanta da kuma kasar baki daya muddin ya zama shugaban kasa.

Bola Tinubu ya bayyana hakan ne yayin magana a wani taro da kungiyoyi masu fada aji na arewacin Najeriya da suka hada da kungiyar dattawan arewa da kuma Arewa Consultative Forum suka shiryawa ‘yan takarar shugaban kasa a Arewa House, a JIhar Kaduna.

Darajar Naira Ta Karu A Kasuwar Canjin Kudi

Tinubu ya ce cikin abubuwan da zai fara yi shine kammala aikin wutar mambilla da aka shafe tsawon shekaru ba tare da yin aikin ba, inda ya ce tashar za ta samar wa da kasar wuta mai karfin megawatt 3,050 da kuma zai kasance daya daga cikin tasha mafi girma a fadin kasar.

“Abin da yake kawo jinkirin kammala wannan aikin shine rashin isassun kudade. Ba mu iya kebe isassun kudade wa manyan ayyuka masu daukar dogon lokaci. Za mu kammala wadannan ayyuka saboda muna zuwa da wani tsari mai kyau ga kasar,” in ji Tinubu.

Advertisement

Ya kuma ce zai kawo masu zuba jari a ciki da kuma wajen kasar wadanda za su kammala aikin da kuma zai kawo wa kasar ci gaba.

Bola Tinubu Facebook

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending