News
NDLEA ta kama mutum 192 da ake zargi da safarar kwaya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar hana sha da safarar miyagun kwayoyi a Najeriya – NDLEA ta kama wasu mutane 192 da ake zargi da safarar kwayoyi tsakanin watan Janairu zuwa Satumba a jihar Ebonyi.
Hukumar ta kwace kwaya da ta kai kilogiram 113 a jihar, kamar yadda kwamandan hukumar Iyke Uche ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na NAN.
Qatar na nuna rashin jin dadi kan maganar ‘yan ci rani
“Mun yi wannan kamen ne a wurare daban-daban a cikin jihar,” in ji Uche.
A bangaren safarar kwayoyi a jihar, babban kwamandan ya ce ba a fiye kasuwancin kwayoyi a jihar ba, kawai dai tana da masu ta’ammali da ita ne da yawa.
Advertisements
