Connect with us

News

Mutum 2 Sun Gurfana A Gaban Kotu Kan Zargin Bata Sunan Ganduje A Wasan Barkwanci

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

A ranar Laraba aka gurfanar da wasu mutum biyu a Kotun Majistare da ke Nomansland a Kano, kan zargin bata sunan Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje.

Advertisement

Bayanan farko sun nuna wadanda ake zargin sun wallafa wani bidiyon barkwanci a dandalin Facebook inda a ciki suka ce Gwamnan ba ya ganin fili ya kyale, kuma wai ya cika barci sosai.

Za A Yi Fama Da Hazo Da Kura A Jihohin Arewa A Kwanaki Masu Zuwa – NiMet

Advertisement

Bayan karanta bayanan farko, wadanda ake kara sun amsa tuhumar da ake yi musu.

Lauyan mai gabatar da kara Barista Wada Ahmad Wada, wanda babban lauya ne a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano, ya nemi a yi masa shari’a a kan mutane biyun da ake kara.

Advertisement

Kotun ta sami mutanen da ake zargin da aikata laifin, ta kuma dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar bakwai ga watan Nuwamba don yanke hukunci.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending