News
Dala na gab da zarta Naira dubu a Najeriya.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Ana fargabar masu karamin karfi na iyan shiga wani yanayi
Darajar Naira ta ci gaba da faduwa a karshen wannan makon, inda a yanzu farashin Pam daya na Ingila ya zarta Naira dubu daya a kasuwannin bayan fage.
An Fara Biyan Malaman Jami’ar Da Suka Balle Daga ASUU Albashinsu Na Wata 8
Ana fargabaar cewa, ita ma Dalar Amurka za ta zarta Naira dubu 1 kowanni lokaci daga yanzu.
A makon jiya ne Hukumar da ke Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya ta kai samame a kasuwannin ‘yan canji a Lagos da Abuja da Kano bisa zargin su da haddasa tsadar farashin kudaden ketare a kasar.
Sai dai ‘yan canjin sun mayar da martini, inda suka ce tsare-tsaren gwammati ne ya jefa kasar cikin halin da take ciki.
Advertisements
