News
KASHI 60 BISA DARI NA YAN AREWA BASU DA ASUSUN AJIYA A BANKI~ Sanata Uba Sani
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Sanata Uba Sani mai wakiltar Jihar Kaduna ta tsakiya Kuma Shugaban Kwamitin shaanin kudade na Majalisar Dattijai, yace Kashi 60% bisa 100% na mutanen Arewa daya kamata su mallaki asusun ajiya a banki basu da shi.
Yayin da su Kuma kudu Kashi 80% cikin 100% na mutanen yankin suna da asusun ajiyar kudade a banki.
Harin Jiragen Sama Ya Kashe ‘Yan Bindiga Da Dama A Kaduna da Zamfara.
Har ila yau Bankin masanaantu na Micro Finance bank, Kashi 80% bisa 100% Yan kudu ne suke da su.
Da yake mayar da martani game da bayanan da suka fita a bayabayan nan kan cewar Yankin kudu sun fi amfana da tallafin rancen kudade da bankin raya kasa yake bayarwa, musamman Jihar Lagos data tashi da kusan Kashi 51% bisa 100% na dukkan kudaden da Gwamnati ta warewa jihohin Kasar nan baki daya.
Uba Sani, yace bazai taba yiwuwa a baka bashi baka da asusun ajiya a banki ba,Sanata Ali Ndume, ne yayi Wannan babatun a lokacin da yake tattauna da yan jaridu, inda yace jihohin Arewa an bar su a baya inda jihohin Kudu suka tashi da kaso Mafi tsoka kan rancen kudaden daga Gwamnati.
Daga karshe Sanata Uba, ya baiwa manyan Arewa Shawarar cewar su Bude bankuna, kazalika Kuma Al’ummar Arewa suyi kokarin bude asusun ajiya a bankuna.
