News
Likita Daya Ne Ke Duba Marasa Lafiya 10,000 A Najeriya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Najeriya (NARD) ta ce karancin likitocin da ake fuskanta a kasar ya yi munin da a yanzu likita daya ne ke duba marasa lafiya 10,000.
Kungiyar ta ce a halin da ake ciki, likitocin da ake da su a fadin kasar nan ba su wuce 10,000 ba.
Ta ce adadin likitocin raguwa yake kullum sakamakon barin kasar da suke yi zuwa aiki a kasashen waje.
Shugaban kungiyar na kasa, Dokta Emeka Orji, ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da jaridar Punch.
A cewarsa, kimanin likitoci 100 ne ke barin kasar zuwa ketare duk wata don neman aiki.
Ya ce, daga cikin likitoci 80,000 da suka yi rajista, kimanin kaso 64 cikin 100 ba sa aiki saboda wasunsu sun yi murabus, wasu sun bar kasar, wasu sun sake aiki, wasu kuma sun mutu.
Shugaban ya kuma ce kafin wannan lokacin, “Likitoci 16,000 ake da su, amma yanzu ba su wuce dubu tara zuwa 10 ba.”
Hakan na nufin likitocin da ake da su da za su kula da al’ummar Najeriya su sama da miliyan 200, ba su wuce guda 10,000 ba.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
