News
Rasha ta yi watsi da tayin tattaunawa tsakanin Putin da Biden
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Fadar Kremlin ta Shugaba Putin na Rasha ta yi watsi da kalaman Shugaban Amurka Joe Biden cewa a shirye yake ya tattauna da Putin ɗin idan har yana son kawo ƙarshen yakin Ukraine.
Mista Biden ya jaddada cewa haka na iya faruwa ne kawai idan sojojin Rasha suka janye daga Ukraine.
Kakakin Kremlin Dmitry Peskov ya ce Rasha ba ta shirya cika waɗan nan ƙa’idojin ba.
A hirarsu ta waya da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, Mista Putin ya bayyana halayyar da ƙasashen Yamma ke nunawa ga Ukraine a matsayin ɓarna.
Ya kuma ya ce ba lalle a je teburin sulhu ba yayin da ƙasashen na Yamma ke bai wa Ukraine dukkanin goyon baya ta fuskar siyasa da kuma kuɗaɗe.
Advertisements
