News
Burkina Faso ta dakatar da rediyon RFI yaɗa shirye-shirye a ƙasar
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin Burkina Faso ta dakatar da gidan rediyon Faransa na Radio France Internationale (RFI) daga yaɗa shirye-shirye a faɗin ƙasar.
A cewar gwamnatin riƙon ƙwaryar ƙasar, RFI ya yaɗa wani saƙon farfaganda na wani shugaban masu iƙirarin jihadi a ranar Asabar.
Sanarwar da aka wallafa a shafukan zumunta na gwamnatin ƙasar ta ce “kafar yaɗa labaran[RFI] ta ba da gudummuwa wajen bai wa ƙungiyar ‘yan ta’addan damar karya gwiwar ‘yan Burkina Faso waɗanda ake ƙarfafa wa gwiwar kare ƙasarsu”.
Ta ƙara da cewa a jiya Juma’a RFI ya sake maimaita wasu bayanai na boge cewa Shugaban Riƙon Ƙwarya Kaftin Ibrahim Traoré ya tabbatar da cewa an yi yunƙurin ƙwace mulkinsa ne a yunƙurin juyin mulkin da aka yi.
Gwamnatin ta ce ta nuna ɓacin ranta a watan da ya gabata game da yadda ‘yan jaridar RFI ke kashe gwiwar ‘yan ƙasa wajen yaƙi da masu iƙirarin jihadin.
A watan Maris ne maƙwabciyar ƙasar, Mali ta dakatar da ayyukan RFI da gidan talabijin na France 24, waɗanda dukkansu mallakar Faransa ne, suna masu zargin su da yaɗa zarge-zargen cin zarafin da sojojin Mali ke yi.

