News
Rundunar sojin sama na ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin ‘yan bindiga a Kaduna.
DAGA MUSLIM YUNUS ABDULLAH
Rundunar sojin saman Najeriya na ci gaba da kai hare-hare kan sansanonin ‘yan bindiga da aka gano da kuma wasu yankunan da ke kewayen jihar Kaduna.
Hakan na cikin sata sanarwar da kwamashinman rkokin cikin gida da tsaro na jihar kaduna Samuel Aruwan yarabawa mane ma labarai
An saki wanda ya kashe jarumin da ya yaƙi wariyar launin fata a Afrika ta Kudu
Sanarwar takara da Cewa Wani martani da gwamnatin jihar Kaduna ta nuna cewa an kai hari tare da lalata wani sansani a Riyawa, karamar hukumar Igabi. An kuma kai hari a wani wurin ‘yan ta’adda a Tofa general a karamar hukumar Birnin Gwari.
An bai wa sojojin kasa da ke aiki a yankunan Maidaro, Dogon Dawa, Damari, Saulawa da Farin Ruwa, a karamar hukumar Birnin Gwari, tallafin jiragen sama na kusa.
An gudanar da aikin leken asiri dauke da makamai a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, Buruku, Kurmin Dande, Damba, Ungwan Yako, Udawa, Manini, Kuriga, Gagafada, Kushaka, Polewire da Kampongi Doka da suka hada da kananan hukumomin Chikun da Birnin Gwari. Ba a ga wani abin tuhuma ba a wuraren da aka rufe.
