News
An umurci mutane su zauna cikin shirin ko-ta-kwana bayan aman dusten Lascar
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Jami’ai a Chile sun gargadi mutane da su zauna cikin shirin ko-ta-kwana bayan da dutsen Lascar ya yi aman hayaki zuwa sararin samaniya.
Dutsen na Lascar dai ke a Andes, ya fara aman hayaki ne jiya Asabar, wanda ya janyo barazanar girgizar ƙasa.
Ba a dai samu asara ba a yankin kawo yanzu, amma an sanya alamun gargadi.
BBC ta rawaito cewa Hukumar kula da harkar ma’adinai da duwatsu, ya ce alamar gargadin na nuna cewa akwai matsala a yankin.
Sai dai, jami’ai na can suna sanya ido domin kare mutane kan barazanar samun fashewa ko tashin hayaki.
-
News22 hours ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
