News
Malaman Jami’o’i a Ghana sun janye yajin aiki
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Malaman jami’o’in Ghana sun janye yajin aikin da suka soma a watan da ya wuce.
Kungiyar malaman da ake kira TUTAG wacce ke wakiltar jami’o’in kasar su 10 ta ce ta janye yajin aikin ba tare da wani bata lokaci ba.
Mutum uku sun mutu bayan ‘yan bindiga sun kai hari a ofishin INEC da ke Imo
A don haka kungiyar ta yi kira ga malamai su koma bakin aiki daga yau Litinin.
Malaman sun shiga yajin aiki ne domin a kyautata musu yanayin aiki sannan gwamnati ta kara musu alawus na gyaran mota.
Yajin aikin ya janyo tsaiko a harkokin ilimi a fadin kasar.
Shugaban kungiyar ta TUTAG, Farfesa Collins Ameyaw ya shaidawa BBC cewa gwamnati ta ce za ta biya kudin alawus-alawus daga watan Yunin badi.eted for this year.
Advertisements
