Connect with us

News

Ana musayar yawu kan tsige shugaban karamar hukuma a Jigawa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Majlisar dokokin jihar Jigawa ta ce majalisar kansilolin karamar hukumar Ringim ba su da hurumin tsige shugaban karamar hukumar.

 

Advertisement

Wannan na zuwa ne bayan da kansilolin suka sanar da tsige shugaban karamar hukumar bisa zarginsa da gudanar da wasu ayyuka ba tare da sanin majalisar ba.

Netherlands ta nemi gafara akan bautar da bakaken fata

Shi ma mutumin da kansilolin ke cewa sun tsige din yace yana nan daram a kan kujerarsa kasancewar ba su da ikon yin hakan.

Advertisement

 

Kansilolin dai sun aikawa majalisar dokokin jihar Jigawa wasika game da abin da suka yi, don majalisar ta dauki mataki na gaba, amma majalisar ta shawarci kansilolin su koma baya su bi tsarin doka, saboda a cewar shugaban kwamitin watsa labaran majalisar ba su tura musu wasika takanas zuwa wurinsu ba, illa dai sun saka sunansu cikin jerin wadanda ake sanar da su an dauki matakin.

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending