News
Sojoji uku sun mutu bayan da jirginsu ya kama da wuta a Nijar
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
A jamhuriyar Nijar wani jirgin sojin kasar ya kama da wuta yayin da yake ƙoƙarin sauka bayan da ya dawo daga wani atisayen soji, lamarin dai ya yi sanadiyar mutuwar sojoji uku.
Rundunar sojin Nijar ɗin ta tabbatar da mutuwar sojin ƙasar biyu da na Ukraine ɗaya – waɗanda duka ma’aikatan jirgin ne – a lamarin da ya faru a filin jirgin saman birnin Yamai.
Kane ya ci ƙwallo a wasan Premier na farko bayan hutun Kofin Duniya
BBC ta rawaito cewa Jirgin ya dawo daga wani atisayen da ya saba yi a lokacin da ya kama da wuta yayin da yake ƙoƙarin sauka a filin jirgin na Yamai.
Kawo yanzu dai hukumomin sojin na Nijar ba su bayyana musabbabin tashin wutar a cikin jirgin ba, sai dai sun ce suna kan gudanar da bincike domin gano musabbabin hakan.
A cikin wata sanarwa da ministan tsaron ƙasar ya sanya wa hannu a madadin shugaban ƙasar ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan mamatan
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
