News
Ɗaliban jami’o’i a Ghana sun koka kan ƙarin kuɗin makaranta
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ɗaliban jami’o’i a ƙasar Ghana sun yi watsi da ƙarin kuɗin makaranta da wasu jami’o’in ƙasar suka yi.
Ƙungiyar Daliban ƙasar ta umarci masu ruwa da tsaki da su hana jami’o’in ƙasar ƙara kuɗin makarantar.
A baya-bayan nan ne dai Majalisar Dokokin ƙasar ta amince da ƙarin kashi 15 cikin 100 na kuɗin makaranta ga jami’o’in ƙasar.
To sai dai ɗaliban na cewa wasu jami’o’in sun yi ƙarin kusan kashi 40 cikin 100, saɓanin abin da majalisar dokokin ƙasar ta amince da shi.
Daliban sun bayyana damuwarsu game da lamarin, yayin da ƙasar ke fama da tsadar rayuwa, da ƙaruwar farashin kayyaki da kusan kashi 50 cikin 100.
Ƙungiyoyin ɗaliban ƙasar sun ce ƙarin kuɗin zai jefa dalibai da iyayensu cikin mawuyacin hali.
Advertisements
