News
Yan sandan Zamfara sun kashe ɗan bindiga, sun kwato makamai
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ta tabbatar da kashe wani dan bindiga tare kuma da kwato makamai a kan hanyar Gusau bayan samun rahoton yunkurin kai hari da ‘yan bindigar suka yi.
A wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu ya fitar, ya ce a ranar 1 ga watan Janairu ne suka samu nasarar fatattakar ‘yan bindigar zuwa cikin daji bayan artabu na tsawon lokaci, inda suka kwato bindigar AK-47 da harsasai 104 da kuma wasu abubuwan yin asiri daga hannun ‘yan bindigar.
Har ila yau, sanarwar ta ƙara da cewa wata rundunarta ta musamman ta kama wasu mutum shida da ake zargi da aikata ta’addanci da garkuwa da mutane da kuma satar shanu, ciki har da wani mai bai wa ‘yan bindiga bayanai da ke ƙananan hukumomin Zurmi da Shinkafi na jihar.
Kakakin ‘yan sandan ya ce wadanda ake zargin na hannun ‘yan sanda, inda suke bayar da bayanai da za su kai ga kamo sauran masu laifi, inda ya ce bayan haka za a tura su zuwa kotu domin yi musu hukunci bayan kammala bincike
