News
Gwamna jihar Yobe ya amince da rage Farashin Sabbin shaguna a sabuwar kasuwar zamani Da Ya Gina
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya amince da rage kashi 35 na hayar shaguna a sabuwar kasuwar zamani da aka kaddamar domin tallafawa da karfafa gwiwar ‘yan kasuwa. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ground Floor Prime View Double da ake bada shi da a farashin farko na N468,000 a kowace shekara yanzu ya zama N304,200 yayin da Ground Floor Prime View Single da farko aka sanya mai N390,000 yanzu N253,500p.a. sabanin shawarar farko da kwamitin jihar kan rabon shaguna ya bayar.
Hakazalika, Ground Floor Prime View mai fuska biyu wanda zai da aka sanya mai farashin N442,000 yanzu ya zama N287,300 a duk shekara, sauran kuma na Ground Floor akan N390,000 yanzu an rage zuwa N253,500. Da dai sauransu.
Advertisements
