Connect with us

News

Yan asalin jihar Yobe sunyi Bikin cika shekaru dari Biyu da shigowar su  Katsina

Published

on

DAGA IDRISS HUSSAINI NGURU

A ranar Asabar 7 ga watan Oktoba 2023 ne Al’ummar Badawa ‘Yan Asalin jihar Yobe, da suka shigo jahar  Katsina tun a karni na 18 kimanin shekaru dari biyu da ashirin da wani abu sukayi bakin tunawa da juna.

Advertisement

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Alhaji Abba Yusuf Funtua shine shugaban al’umar Badawa Yan jihar Katsina, kuma shugaban taro, a madadin Al’umar ta Badawa ya gabatar da jawabin maraba da bakin da suka shigo jihar Katsina da Badawa na jihar Katsina.

Majalisar Dokokin KanoTa Amince Da Kasafin Kudi Na Naira Biliyan N58

Manyan Baki da suka halarci taron akwai, Sardaunan Bade, tsohon shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Dakta Ahamad Lawan, da tawagar sa, tsohon Ministan Jiragen Sama na Nijeriya Alh. Hadi Sirika, Al’ummar Badawa daga Jihar Yobe, Hakimman Masarautar Katsina, da na Yobe, Muƙarraban Gwamnatin jihar Yobe da sauran su.

Advertisement

Manyan Malamai Furofesoshi da jami’o,in Najeriya suka gudanar da Kasidu a wajen taron, inda wasunsu suka bayyana Asalin Al’ummar Badawa, Tarihin su, da kuma Kafuwar Sarautar su.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending