News
Majalisar Dokokin KanoTa Amince Da Kasafin Kudi Na Naira Biliyan N58
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Majalisar dokokin jihar Kano, ta amince da kasafin kudin shekarar 2023, wanda hakan ke nuna wani gagarumin ci gaba ga ayyukan ci gaban jihar.
Zauren majalisar wanda shugaban majalisar, Rt Hon Jibril Ismail Falgore ya jagoranta, ya amince da tsarin kasafin ne bayan nazari sosai da kwamitocin majalisar baki daya suka gudanar.
Majalisar dokokin Kano ta karrama direban adaidaita sahun da ya tsinci kudi ya mayar da kyautar kudi
Manufar wannan kasafin kudin ita ce, samar da tsarin kudi da ya dace don aiwatar da wasu ayyuka masu tasiri a fadin jihar, dai-dai da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 (kamar yadda aka gyara).
Gwamnan Abba Kabir Yusuf ne ya mika kudurin kasafin kudin ga majalisar domin ta duba tare da amincewa tun kwanakin baya.
Tsarin kasafin kudin ya haura sama da Naira biliyan N58, an ware kashi 92 cikin 100 domin aiwatar da ayyukan raya kasa da walwalar al’ummar jihar yayin da aka ware ragowar kashi 8 domin gudanar da ayyuka masu bijirowa na yau da kullum.
A Wani labarin kuma Majalisar dokokin Kano ta karrama direban adaidaita sahun da ya tsinci kudi ya mayar da kyautar kudi
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
