Connect with us

News

Kotun Kano Ta Daure Alkalai Kan Badakalar Kudin Marayu N99m

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA

 

Advertisement

 

Wata Kotun Majistare mai lamba 14 ta aike da wasu alkalai da ma’aikatan Hukumar Shari’a gidan gyaran hali saboda zarginsu da wawure Naira miliyan 99.

Advertisement

 

Kotun, karkashin Mai Shari’a Mustapha Sa’ad Datti ta aike da mutanen ne bisa zargin su da yin sama da fadi da kudaden wadanda mallakin wasu marayu ne.

Advertisement

Janyewa daga takara a yanzu ‘rashin kishin ƙasa ne’ – Rabi’u Musa Kwankwaso

Tun da farko dai Hukumar Karbar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ce ta gurfanar da wasu alkalai da kuma ma’aikatan Hukumar Shari’ar Musulunci a gaban kotun.

 

Advertisement

Wadanda aka gurfanar a gaban kotun sun hada da Sani Ali da Sani Uba Ali da Bashir Baffa da Gazzali Wada da Hadi Tijjani Mu’azu da Alkasim Abdullahi da Yusuf Abdullahi da kuma Mustafah Bala.

 

Advertisement

Sauran sun hada da Jaafar Ahmad da Adamu Balarabe da Aminu Abdulhadi da Abdullahi Sulaiman Zango da Garba Yusuf da Bashir Ali Kurawa da kuma Usaina Imam.

 

Advertisement

Takardar karar ta bayyana cewa ana tuhumar alkalan da ma’aikatan shari’ar da laifin hada kai da cin amana da satar Naira miliyan 99, laifukan da dukkaninsu suka musanta.

 

Advertisement

Mai gabar da kara, Barista Zaharaddin Kofar Mata, ya roki kotun da ta ba su wata ranar domin sake gabatar da su a gaban kotun tare da kawo shaida.

 

Advertisement

Sai dai lauyoyin wadanda ake kara bakinsu ya zo daya a kan neman beli, kodayake kotun ta ki ta bayar da belin nasu, inda ta ce za ta bayyana matsayinta game da rokon belin a zamanta na gaba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending