Connect with us

News

Yan bindiga sun kai hari ofishin ‘yan sanda

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA 

 

 

An kashe wani jami’in ‘yan sanda guda a dare ranar Juma’a, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari wani ofishin ‘yan sanda da ke karamar hukumar Oguta a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya.

 

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wasu ‘yan sanda sun farmaki ‘yan bindigar lokacin da suke kan aikinsu.

Advertisement

Kwamitin majalisar dattijai ya kira shugaban NNPC kan kwangilar naira biliyan 48

Bayan kashe jami’in ɗan sandan, an ruwaito cewa ‘yan bindigar sun tsere da raunuka a jikinsu.

 

Jaridar ta ruwaito cewa, da zuwan maharan suka harba wani abin fashewa cikin ofishin ‘yan sandan sannan suka buɗe wuta kan jami’an da ke bakin aiki.

 

Kakakin ‘yan sanda a jihar, Henry Okoye, ya tabbatar da harin amma yace an daƙile harin ‘yan bindigar.

 

Advertisement

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending