Connect with us

News

Kano: NDLEA ta kama makaho da kuturu dauke da muggan kwayoyi.

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Hukumar Yaki da masu sha da safarar miyagun kwayoyi a Najeriya ta NDLEA ta sake bayyana matukar damuwa akan yadda ‘yan Najeriya ke ci gaba da hada hada da kwayoyi cikin su harda makafi da kutare.

 

Advertisement

Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi yace jami’ansu sun yi nasarar kama wani dattijo makaho mai shekaru 67, Aliyu Adebiyi a Jihar Osun, wanda aka samu da kilogram 234 na tabar wiwi a gidansa, yayin da aka kuma kama wani kuturun da ake kira Haruna Abdullahi mai shekaru 45 a Garko dake Jihar Kano da sama da kilogram 2 na tabar wiwi da kuma wasu nau’o’in kwayoyin da suka hada da diazepam da exol.

Kungiyar Gwale Student Association ( gwalsu ) Ta Gudanar da Sahihin zaben Shugabancin Kungiyar

Kakakin hukumar ya kuma bayyana kama wani matashi Eze Christian Ikenna mai shekaru 42 wanda yayi safarar hodar ibilis da ta kai sama da kilo 16 daga Brazil zuwa tashar jiragen Enugu.

Advertisement

 

Babafemi ya kuma ce jami’an hukumar sun yi nasara kama tramadol dubu 60 daga wani dillali da ake nema ruwa ajallo a unguwar Bariga dake Lagos da ake kira Diugwu Alphonsus.

Advertisement

 

NDLEA ta gargadi ‘Yan Najeriya da su kaucewa sanya hannu a aikin safarar kwayoyi da kuma dillancin ta, domin doka za tayi aiki akan duk mutumin da ya fada komarsu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending