Connect with us

News

PDP Kano: Kotu Ta Gargadi Wada Sagagi ya daina bayyana kansa a matsayin shugaban jam,iyar

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

 

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta bayar da sanarwar sakamakon bijirewa umarnin kotu a kan wanda ake kara, Shehu Wada Sagagi, kan bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na Kano.

 

Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa kwamitin riko na jam’iyyar PDP reshen jihar Kano, a ranar Asabar din da ta gabata, ya zargi tsohon shugaban rusassun shugabannin jihar, Shehu Sagagi, da kin bin umarnin kotu inda ya bayyana kansa a matsayin shugaban riko.

Advertisement

PDP ta zargi Tinubu da yin safarar miyagun kwayoyi zuwa kasashen waje.

 

Sakataren kwamitin riko na jam’iyyar PDP, Bala Aliyu ne ya bayyana hakan a Kano, yayin da yake zantawa da manema labarai akan abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar PDP anan Kano, inda ya jaddada cewa babu wani bangare a jam’iyyar.

 

 

 

 

Advertisement

 

Ya ce kwamitin ya shigar da kara ga ‘yan sanda da ma’aikatan gwamnatin tarayya kan aikata laifin da Sagagi ya aikata, wanda ke iya haifar da rashin zaman lafiya a jihar Kano.

 

 

A baya dai PDP ta kai karar Shehu Wada Sagagi, Bashir Tanko Mohammed, Ali Tijjani Ansaru Gambo Jamil Abba zuwa kotu, .

 

Advertisement

 

 

 

Don haka a karar da ta shigar PDP a matsayin wanda ake bin sawun shari’a da Shehu Wada Sagagai, wanda ake kara/mai kara, babbar kotun tarayya a ranar 9 ga Janairu, 2023 ta yi gargadin cewa Sagagi ya daina bayyana kansa a matsayin shugaban jam,iyar, don haka zai kasance da laifin cin mutunci. kotu kuma za a kai shi kurkuku.

 

Sanarwar ta ce: ”Ku lura cewa sai dai idan kun bi umarnin da ke kunshe cikin wannan umarni na Kotun Daukaka Kara, don sanin:” Saboda haka hukuncin kotun da ke kara mai lamba NoFHC/ABJ/CS/393/2022 da aka bayar a ranar 25 ga wata. /05/2022 na Taiwo O. Taiwo .J ta kebe a gefe kuma an soke karar FHC/ABJ/CS/393/2022 da aka shigar a ranar 25/032022.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending